8 Satumba 2025 - 23:38
Source: ABNA24
Kasar Yemen Ta Mayar Da Maulidin Manzon Allah A Matsayin Wani Yunkuri Na Fuskantar Isra’ila

Babban birnin kasar Yemen, Sana'a, da sauran lardunan kasar sun gudanar da gagarumin bukukuwa na tarihi na ranar 12 ga watan Rabi'ul Awwal don tunawa da maulidin manzon Allah {SAWA}.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti (A.S.): Babban birnin kasar Yemen, Sana’a, da sauran lardunan kasar sun gudanar da gagarumin bukukuwa na tarihi na ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal na tunawa da ranar haihuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa’Aihi Wasallama.

Miliyoyin jama'a sun yi tururuwa zuwa dandalin Sab'een babban birnin kasar da kuma wuraren da ke kewaye da shi, inda suka yi kayata tare da zana hoton "Muhammadiya". Wannan ya tabbatar da aniyarsu ta bin tafarkin Annabi, da taimakon wanda aka zalunta, da koyi da dabi’unsa na Alkur’ani wadanda suka jagoranci fitar daa bil’adama daga duhu zuwa haske.

Wannan taro mai girma ya kunshi zurfafa alaka tsakanin al'ummar Yemen da Annabi Muhammad (saw) wanda ya zamo manzo ne na al'ummah da bil'adama. Hakan ya dauki hankulan duniya, musamman ma kasar Isra'ila, wanda tuni take firgita da futowar al’ummar Sana'a don nuna goyon bayansu ga Gaza duk ranar Juma'a.

Tabbas Bukin maulidin manzon Allah a kasar Yemen, musamman ma ta fuskacin kungiyar Ansarullah, yana da tasiri da dama ga sahyoniyawa, wanda wannan tasirin ya wuce bangaren addini, ya hada da siyasa, dabarun shugabanci, da tsaro.

Sakon bukin maulidin Annabi zuwa ga “Isra’ila” shi ne cewa rikici ba na siyasa kadai ba ne, har ma da addini da wanzuwa. Wannan dai wani lamari ne da ke nuna matukar damuwa ga gwamnatin mamayar Isra'ila da ke sa ido kan taruwar wadannan jama'ar duk da hare-haren da ta kaiwa ta sama a birnin San'a. Tasirin hare-haren ta sama kan wadannan jama'a yana da iyaka baya da wani tasiri; a maimakon haka, harin na karfafa kudurin Yamanawa na tsayawa tsayin daka tare da Palasdinu da sabunta goyon bayansu ga manufarta.

Ban da haka kuma, goyon bayan da jama'ar ke bayarwa, wanda ke kunshe cikin bayanan goyon bayan Falasdinu, na taka rawa wajen ci gaba da kai hari kan sojojin mamaya na Isra'ila a cikin yankunan da ta mamaye da kuma cikin teku. Wannan ya zama wani nauyi ne mai muhimmanci ga Yemen, tare da kara rubanyar wahalhalu ga Isra’ila wajen fuskantar tsayin daka da hadin kai.

Haramtacciyar kasar Isra'ila ta mayar da hankali sosai kan bukukuwan addini a kasar Yemen, musamman ma maulidin manzon Allah. Hakan ya fito fili a cikin labaran da kafafen yada labaran Isra’ila suka yi kan taron.

Jaridu irin su Yedioth Ahronoth da Jerusalem Post da kuma tashoshi irin su Kan da 24 sun mayar da hankali kan bikin, inda suka nuna dimbin jama’a da yadda suka jama’a suka halarta.

Sa ido kafafen yada labarai na Isra'ila kan yadda ake gudanar da bukukuwan Maulidi wani bangare ne na dabarun tsaro don sa ido kan karfin abokan gaba da fahimtar tushen rikice-rikice a yankin.

Kafofin yada labaran Isra'ila na kallon bukukuwan Maulidi a matsayin dandalin bayanai na kyamar sahyoniyawa. Haaretz ta mayar da hankali ne a kan wata sanarwa da daya daga cikin malaman da suka halarci taron ya yi, inda ya ce: "Yemen ta fi kowace kasa shiri don mayar da addinin Musulunci tushensa bisa albarkacin makarantar kur'ani mai tsarki".

Maariv ta mayar da hankali ne kan dimbin fitowar jama'a a birnin Sana'a, tana mai kallon bikin a matsayin wani abin da ke nuni da irin yadda kungiyar Ansarullah ta ke da karfi. An yi nuni da cewa jawaban sun hada da hare-haren da ake kaiwa Isra’ila da Amurka, kuma sun bayyana taron a matsayin wani nuna mai karfi na siyasa maimakon na addini.

A nata bangaren, jaridar Yedioth Ahronoth ta alakanta bikin da rikicin yankin, inda ta yi nuni da cewa, kungiyar Ansarullah ta yi amfani da wannan dama wajen baje kolin makamansu na soja da na siyasa, ciki har da rera taken nuna adawa da Isra'ila da kiraye-kirayen goyon bayan gwagwarmayar da ake yi a Gaza.

A takaice dai kafafen yada labaran kasar Isra'ila sun bayyana bikin maulidin manzon Allah a matsayin wani gagarumin baje kolin karfi da ci gaba a fagen fito na fito da mamaya.

Ta yi nuni da cewa, al'ummar kasar Yemen sun gudanar da bukukuwan a cikin wani yanayi da ba a taba ganin irinsa ba, tare da daga korayen tutoci da kuma cunkoson jama'a a dandalin. Ta dauki wadannan hotuna a matsayin mai dauke da "sakon jama'a kai tsaye da sakonnin siyasa" ga masu sauraron gida da na waje.

Kafofin yada labaran kasar Isra'ila sun bayyana cewa, al'amuran da suka biyo bayan wannan lokaci sun tabbatar da cewa al'ummar kasar Yemen sun canja taron maulidin manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa’alihi Wasallam daga gudanar da bukukuwan addini zuwa wata munasaba ta gangamin jama'a da sakon bijirewa, a daidai lokacin da sojojin Yaman ke ci gaba da kai hare-haren makami mai linzami da jirage masu saukar ungulu a kan haramtacciyar kasar Isra'ila don nuna goyon baya ga Gaza.

Kafofin yada labaran Isra'ila sun jaddada cewa wadannan al'amura sun nuna "hadin kai da tsayin daka na matsayin Yemen," duk da yunkurin da ake yi na kara ruruwar kai masu hare-hare da matsin lamba.

Babban abin da ya fi bawa Isra'ila tsoro game da bikin maulidin manzon Allah a birnin San'a, tasirin dan hakan zai haifar ga yunkurin daidaita alakarta da wasu kasashen Larabawa.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha